Competition in this pair is now closed, and the winning entry has been announced. Discussion and feedback about the competition in this language pair may now be provided by visiting the "Discussion & feedback" page for this pair. Entries may also be individually discussed by clicking the "Discuss" link next to any listed entry. Source text in English A theme of the age, at least in the developed world, is that people crave silence and can find none. The roar of traffic, the ceaseless beep of phones, digital announcements in buses and trains, TV sets blaring even in empty offices, are an endless battery and distraction. The human race is exhausting itself with noise and longs for its opposite—whether in the wilds, on the wide ocean or in some retreat dedicated to stillness and concentration. Alain Corbin, a history professor, writes from his refuge in the Sorbonne, and Erling Kagge, a Norwegian explorer, from his memories of the wastes of Antarctica, where both have tried to escape.
And yet, as Mr Corbin points out in "A History of Silence", there is probably no more noise than there used to be. Before pneumatic tyres, city streets were full of the deafening clang of metal-rimmed wheels and horseshoes on stone. Before voluntary isolation on mobile phones, buses and trains rang with conversation. Newspaper-sellers did not leave their wares in a mute pile, but advertised them at top volume, as did vendors of cherries, violets and fresh mackerel. The theatre and the opera were a chaos of huzzahs and barracking. Even in the countryside, peasants sang as they drudged. They don’t sing now.
What has changed is not so much the level of noise, which previous centuries also complained about, but the level of distraction, which occupies the space that silence might invade. There looms another paradox, because when it does invade—in the depths of a pine forest, in the naked desert, in a suddenly vacated room—it often proves unnerving rather than welcome. Dread creeps in; the ear instinctively fastens on anything, whether fire-hiss or bird call or susurrus of leaves, that will save it from this unknown emptiness. People want silence, but not that much. | The winning entry has been announced in this pair.There were 4 entries submitted in this pair during the submission phase. The winning entry was determined based on finals round voting by peers.
Competition in this pair is now closed. | Wani batu da ya daɗe, musamman a ƙasashen da suka ci gaba, shine mutane na neman rashin hayaniya amma sun gaza samu. Rugugin matafiya, ƙarar wayoyin hannu wanda baya ƙarewa, sanarwa ba ƙaƙƙautawa daga nau'rori a motocin bas bas da jiragen ƙasa, kwarmaton talabijoji har a ofisoshin da babu kowa, lamari ne da ke haifar da rashin jin daɗi. Ɗan adam na wahar da kansa da yawan hayaniya duk da cewa yana bukatar kishiyar haka—a cikin daji ne, cikin kogi da wuraren shaƙatawa da aka keɓe domin samun nutsuwa da kwanciyar hankali. Alain Corbin, wani farfesan tarihi, ya rubuta daga mafakarsa dake Sorbonne, da kuma Erling Kagge, wani mai bincike ɗan ƙasar Norway, wanda yayi rubutu a kan abubuwan gani da ido da ya gani, sun yi tsokaci daga wurin da suka yi ƙoƙarin fidda jaki daga cikin duma. To amma, kamar yadda Mista Corbin ya ambata a cikin wani littafi mai suna "A History of Silence", babu maraba tsakanin dambe da faɗa a kan yadda surutu yake a da da kuma yanzu. Kafin shigowar tayoyin mota, titunan birane sun cika da ƙarar tayoyin ƙarfe da kuma kofaton dawakai a kan duwatsu. Kafin woyayin hannu su zama ƙarfen ƙafa, motocin bas bas da jiragen ƙasa su ke zuba ɗan karen surutu. Hatta masu sayar da jaridu ba a barsu a baya ba wurin tallata hajarsu a fili tamkar dai yadda masu sayar da kayan marmari kan yi. Gidajen wasan kwaikwayo da makaɗa sun zamarwa mutane larura. Harma a gefen gari, zaka ji masu aikin ƙarfi na waƙe-waƙe lokacin da suke aiki. Amma yanzu ba sa yi. Abinda ya sauya ba yawan surutu bane, wanda aka yi kuka da shi a zamanin da, amma yadda abin ya ɗauki sabon salo dangane da yadda surutu ya mamaye duk wani wuri da ya kamata a sami rashin hayaniya. Babban abin ta'ajibi shine yadda suruta ya mamaye ƙungurmin daji, cikin hamada har ma da ɗakin da babu kowa—babu yadda za a yi maraba da hayaniya a waɗannan wurare. Wanda maciji ya sara in ya ga tsumma sai ya tsorata. Surutun da bai kai ya kawo ba kamar hucin wutar da aka kunna, kukan tsuntsu, ko motsin ganyen bishiya sai ya sa fatar kunne ta ƙara kauri domin kare kanta daga abinda yaka je ya zo. Mutane suna son rashin hayaniya amma basu nuna da gaske suke ba. | Entry #23086 — Discuss 0 — Variant: Not specifiednone
Winner Voting points | 1st | 2nd | 3rd |
---|
22 | 4 x4 | 2 x2 | 2 x1 |
| Maudu'in zamani, akalla a kasashen da suka cigaba, shine cewa mutane suna bukatar rayuwa ta rashin hayaniya ko kara amma sun kasa samun hakan. Karar ababen hawa, karar sautukan wayoyi ba kakkautawa, sautukan na'urorin sanarwa a cikin motocin bas da jiragen kasa, karar akwatunan talbijin hatta a cikin ofisoshin da ba kowa, al'amura ne masu cusgunawa da dauke hankali. Bil'adama suna kashe kansu da karar sautuka don haka suke muradin samun kishiyar hakan - ko dai a cikin dazuka, akan fadin kogi ko kuma a wasu wuraren kebancewa da aka ware don nutsuwa da tsaida hankali. Alain Corbin, wani Farfesa a fannin tarihi, ya kan yi rubuce rubucensa ne daga mafakarsa da ke cikin Sorbonne, da kuma Erling Kagge, wani mai yawon bincike dan kasar Norway, daga labaran yawonsa na barnar Antarctica, wurin ne su duka biyun suka yi kokarin tserewa zuwa can. Amma duk da haka, kamar yadda mista Corbin ya bayyana a cikin "Tarihin Yanayin Shiru," watakila babu wata karar sauti fiye da yadda ta ke a da. Kafin zuwan tayoyin da ake bugawa iska, titunan birane cike suke da karar karafunan kafafun mota da takalman dawakai akan dutse. Kafin kebewa ta sa-kai a wayoyin hannu, motocin bas da jiragen kasa sun kasance wuraren hira da zantuttuka. Masu sayar da jarida ba jibge kayansu suke wuri daya su yi shiru ba, sai dai suna tallarsu ne da sautin murya mai karfi, kamar yadda su ma masu sayar da cheri, furannin violets da kuma danyen kifi suke yi. Gidajen wasan kwaikwayo da dandamalan wakoki da wasanni sun kasance wajen iface ifacen hayaniya da hargowa. Hatta a yankunan karkara, talakawa manoma kan rera waka yayin da suke kaftu. Amma yanzu ba sa yin waka. Dan canjin da aka samu bai kai ko kusa da matsayin hayaniyar karar ba, wadda aka yi ta kuka da ita a karnonin da suka gabata, amma matsayin dauke hankalin mutane, wanda ya ke cike sararin da yanayin shiru zai iya wanzuwa. A nan akwai abin mamaki, saboda idan idan ya kutsa ya mamaye - a cikin kungurmin daji, a cikin tsagwaron hamada, a cikin dakin da aka kaurace masa - da yawa ya kan kasance mai cusgunawa maimakon abin da ake so. Daga nan sai tsana ta shigo; kunne zai rufe ga sauraron kowane abu, koda kuwa hucin wuta ne ko kukan tsuntsaye ko kuwa kasau kasau din ganye da zai fitar da shi daga wannan bakon holoko. Mutane suna son yanayin shiru, amma ba mai tsanani irin wannan ba. | Entry #22892 — Discuss 0 — Variant: Not specifiednone
Voting points | 1st | 2nd | 3rd |
---|
19 | 2 x4 | 4 x2 | 3 x1 |
| Ya zama gama-gari, a kalla a kasashe masu tasowa, cewar mutane na bukatar karancin karar sauti, abinda ya gagare su samu. Karar ababen hawa, kararrakin wayoyi ba kakkautawa. Sanarwa cikin lasifikoki a motocin bus da jiragen kasa, sautin talabijin a cikin ofisoshi da ba kowa, wadannan abubuwa na cuskunawa da dauke hankula. Dan Adam na gajiyar da kansa da kara iri-iri, sabanin abinda ransa ke bege – walau a cikin daji ne, ko a bakin teku ko wani kebabben wajen shakatawa don samar da nutsuwa. Alain Corbin farfesa na tarihi ya rubuto daga inda ya kebe kansa a garin Sorbonne, da kuma Erling Kagge, dan yawon duniya, wanda cikin abubuwan da ya ke tunawa na nahiyar Antarctica, inda su biyun su ka yi kokarin tserewa daga can. Duk da haka, kamar yadda Mr Corbin ya fada a cikin littafinsa me suna “Tarihin Shiru” ya ce watakila ana zuguguta yawan kararrakin da ake dasu. Kafin kirkirar tayoyin da ake buga wa iska, titunan garuruwa cike su ke da kararrakin karafuna na wiluka na karfe da kofatan karfe na dawaki. Kafin bazuwar waya da ta samar da kadaicewa, cikin motocin bus da jiragen kasa cike suke da surutan jama’a. Masu saida jaridu ba zube su suke a kan tebur ba, sai sun kwala muryoyinsu su na talla, kamar yadda masu saida yayan itace iri-iri ke yi. Gidajen wasan kwaikwayo a hargitse su ke da fito da hayaniya. Ko da a kauyuka, manoma na aiki cikin wake-wake. Amma yanzu ba sa yi. Abinda ya canza ba yawan karar sautukan ba ne, wadanda aka yi fama da su daruruwan shekaru a baya, saidai yawan jan hankalin, wanda ke musanya abinda kara zata maye gurbinsa. Akwai kuma wani abun wanda idan ya fado- a tsakar rukukin daji ne, ko a shararriyar Hamada, ko a dakin da ba kowa- yana razanarwa maimakon a yi masa maraba. Tsoro na saukowa, ana kasa kunnunwa don jin komai, hucin wuta ne ko karar tsuntsu ko motsin ganyaye, shine abinda zai cece shi daga wani holoko da ba a sani ba. Mutane na bukatar shiru amma ba irin wannan ba. | Entry #22700 — Discuss 0 — Variant: Not specifiednone
Voting points | 1st | 2nd | 3rd |
---|
15 | 1 x4 | 4 x2 | 3 x1 |
| Wani al'amarin zamani, mussaman a kassache da su ka tchi gaba , shine bukar shiru amma kuma mutane bâ su saminshi KO kadan.Rugumutsin zirgazigan hangna, karan talho, karawrawar na'ura tchikin bus d'à jirgin kassa, talavizo da ke ta kara hal a tchikin offis kin d'à bâ kowa , kururuwa ne da abin shagali bâ iyaka.Mutane a dunyia sun gaji da kara iri iri hal sun kay ga bukatar abin da bâ shi ba , ko a dajine, ko a huadin teku ne, ko a in da a ka jangne din a huta kuma a nutsu ne. Alain Corbin ,malamin tarihi ne ya rubuta a mafakarshi ta Sorbonne, da kuma Erling Kaggae, wani dan yowon buntchike na kassar norway,tchikin tunanin shi na jibji a Antartica, inda su biyu dukan su su ka nemi su huta. Amma hua kuma kamar yadda Malam Corbin ya jaddada a tchikin " Tarihin shiru", wa ta kila wannan zamani bay hi wantchan yawan kara bâ. Kamin a samu tayar roba, titi na tchike da karan tayar karfe mai Kache kunuwa da kuma karfe a kohuatan dawaki su na tafia kan dutsi. Kamin celula y'a kawo sawkin kawyantchewar yarda, bus da jirgin kasa tare su ke kara dà hirar mutane. Ma su sayda jarida bu su bar jarudu bâ a jibgue bâ magana. A-a, ihu su ke da dukka karhin su dan su bada labarin abin da jaridu su ka kumsa ,kuma hakane ma da ma su sayda kayan garka.Wasan koykwayo ma gurin dan karan dumi ne. Hal a gonakay manoma waka suke da karhi kamar sun huada rami. Yau bâ su waka haka. Abin bambamtchin bâ way yawan kara bane bâ Wanda ko mutanen karnaey da su ka shige sun yi kukan shi aman yawan shagaluluwa da suka mamaye gurin da shiru y'a kamata ya shiga.Aman akoy wani abun damua sabo d'à in ya tchika sarkakiar dagin kirya,ko hamada in d'à bâ komay, ko wani daki da a ka bari zama daya, to say ya zama abin ki kuma , ba abin so bâ. Say tsoro ya shigo; kunuwa su na kama duk komi su ka ji da ga hutchin wuta , zuwa wakar tsuntsaye ko motsin tohon itche da zay raba shi da wanan shiru da bay saba bâ. Lalle mutante na bukatar shiru aman hua bâ haka bâ. | Entry #23821 — Discuss 0 — Variant: Not specifiednone
Voting points | 1st | 2nd | 3rd |
---|
8 | 1 x4 | 1 x2 | 2 x1 |
| | | | | X Sign in to your ProZ.com account... | | | | | | ProZ.com translation contestsProZ.com translation contests offer a fun way to take a break from your normal routine while testing and honing your skills with fellow translators.
ProZ.com Translation Contests. Patent pending. |